Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Samun Mata A Mulki Zai Samar Da Ingantacciyar Dimokaradiyya – Kamala Harris


Kamala Harris
Kamala Harris

A jajiberin ganawarta da shugabar kasa mace daya tilo a Afirka, mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris ta fadi ranar Laraba cewa samun karin mata kan karagar mulki wani muhimmin mahadi ne na ingantacciyar dimokaradiyya.

Ganawar ta na zuwa ne a daidai lokacin da fadar White House ke gudanar da taron koli na dimokaridiyya karo na biyu a birnin Washington.

Harris ta ce a lafiyayyen tsarin dimokuradiyya, ya kamata kasancewar mata a madafun iko ya zama ruwan dare gama gari, ba wani abu da ba a saba gani ba da ke zama wani abin labari, kamar yadda hawanta ya kasance.

Yayin da take shirin ganawa da shugabar Kasar Tanzaniya Samia Suluhu Hassan a ranar Alhamis, ta yi magana da mata ‘yan kasuwa da shugabanni a babban birnin kasar Ghana, inda ta yi shelar bayar da tallafin sama da dala biliyan $1B don kamfanoni masu zaman kansu don ciyar da tattalin arziki mata gaba a Afirka.

Bayan haka, da take amsa tambaya daga Muryar Amurka, Harris ta ce shugabancin mata yana da ginshikin samun ingantacciyar dimokuradiyya, kuma batu ne da ta kan gabatar da shi a manyan tarurruka.

"A duk tattaunawar da nake yi da kusan kowane shugaban duniya, wannan batu ne da muke tadawa saboda mun yi imanin cewa yana da mafi kyawun ci gaban wadata da tsaro ga duniya," in ji ta.

Kuma, in ji ta, ba batun tura mata kan karagar mulki ba ne - a cikin ingantacciyar dimokuradiyya, yawancin 'yan kasa za su sami karfin gwiwa, kuma mata da yawa za su jajirce zuwa ga babban mukami.

XS
SM
MD
LG