Kalamun da Edwin Clark yayi na cewa shugaba Jonathan ya cire gwamnonin jihohin dake cikin dokar ta baci ya maye gurbinsu da kantomomin soja na jawo sun kawo muhawara
WASHINGTON, DC —
Yayin da al'ummar jihohin Adamawa da Borno da Yobe ke jiran shugaba Jonathan ya cire masu dokar ta baci da ya kakaba masu shekara daya da ta wuce sai gashi Edwin Clark wanda ake gani a matsayin uban gidan shugaban kasa yana neman a tsige gwamnonin a saka kantomomin soja.
Kalamun dan Niger Delta Edwin Clark inda ya kira shugaban kasa ya cire gwamnonin Adamawa, Borno da Yobe kana ya maye gurbinsu da kantomomin sojoji suna jawo muhawara tsakanin wadanda suke ganin kalamun daidai ne da wanda suke son a yi watsi da su. Clark wanda yana cikin taron kasa ana ganinsa a matsayin uban gida ga shugaban kasa a siyasance.
Edwin Clark ya kara kushewa gwamna Murtala Nyako na jihar Adamawa wanda ya zargi shugaba Jonathan da fakewa da yaki da ta'adanci yana yiwa al'ummar arewa kisan kare dangi. Gwamna Nyako yace yana nan daram kan matsayinsa duk da cewa wasu gwamnonin masu danyen ganye da Jonathan irinsu gwamnan Neja Babangida Aliyu da suna ganin matsayin Nyakon ba daidai ba ne.
Amma ga wasu 'yan PDP da jihohinsu ke cikin dokar ta baci irin su Ado Buni Yadi suna ganin kiran da Clark din yayi daidai ne. Yace a kawo sojoji su gyara kasar sa'an nan a dawo da dimokradiya. Ya kara da cewa idan an cire gwama Kashim Shettima na Borno ba'a kyauta masa ba. Gwamnan yana kokari saidai jihar tana da fadi da yawa kuma bashi da mai taimako. Kowa ya gudu ya kaura zuwa Abuja. Ban da shi gwamnan babu wani babban mutum da matarsa tana Maiduguri. Gwamnan ya bar gidan gwamnati ya koma gidansa na kansa. Da ya ji kiris zai je wurin ya kai gudummawa. Garin da aka kone ya sake ginashi. Kowa aka cuta zai taimakeshi.
Dangane da Yobe yace idan Dr Yerima ya zama gwamna ba za'a sake jin wani tashin hankali ba. Haka kuma Garba Umar na Taraba da Dankwambo na Gombe suna iyakar kokarinsu domin haka suma a barsu. Yace duk wadanda suke kokari shugaban kasa ya yaba masu ba wadanda za'a basu nera biliyan ashirin su bar jam'iyya ba.
To saidai shugaban kwamitin 'yan sanda na majalisar wakilai wanda shi ma dan PDP ne Barrister Usman Bello ya yi watsi da matsayin na Clark. Yace Clark ba dattijo ba ne. Tsoho ne kuma ba dan siyasa ba ne. Haramun ne a ce an jire gwamnonin Adamawa da Borno da Yobe da 'yan majalisunsu. Idan ana zargin gwamnonin da rashin kawo zaman lafiya shin shi shugaba Jonathan ya kawo wa kasar zaman lafiya. A cikin kundun tsarin Najeriya tsaro baya hannun gwamnoni. Yana hannun shugaban kasa ne.
Ga rahoto.

Your browser doesn’t support HTML5