Jami’ai da sauran ‘yan kasa na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu dangane da kalaman rashin mutunci da ake zargin shugaban kasa Donald Trump da furtawa lokacin da yake nuna adawarsa ga ‘yan kasar Haiti da kuma ‘yan ci rani daga kasashen Afirka.
Ranar Alhamis ne shugaba Donald Trump ya baiwa ‘yan Majalisa mamaki lokacin da suke tattaunawa kan shige da fice a fadar White House, “me yasa ake barin dukkannin mutanen da suka fito daga wulakantattun kasashe suka shigo nan?” Trump ya tambaya, a cewar rahotanni masu yawa wadanda kuma aka tabbatar daga mutanen da suka halarci tattaunawar.
Kashi casa’in da biyar na mutanne Haiti bakaken fata ne, haka kuma yawancin mutanen Afirka.
Trump ya ce kamata yayi Amurka ta bar mutane su shigo daga kasashe irin su Norway, wadanda ya bayyana da cewar mafiya yawan su farar fata ne.
Trump yayi amfani da kafar Twitter ranar Juma’a wajen musanta yin amfani da irin wannan kalamai, da ake ‘dauka kamar cin kashi, yace yayi amfani da kalamai masu nauyi, amma bai yi amfani da lafanin da ake zargin yayi ba.