Gwamnan jihar Hawaii ta Amurka, David Ige, ya ce ba za a lamunta da irin kuskuren nan da aka yi na yin gargadin cewa makami mai linzami na nan tafe zuwa Hawaii ba.
Da yammacin jiya Asabar Ige ya fadawa manema labarai cewa yayi takaicin al’amrin kuma ransa ya baci. Ya ci gaba da cewa “Yau rana ce da ba zamu taba mantawa da ita ba – rana ce da aka gaya musu abin da suka fi jin tsoro a duniya na dab da faruwa.”
Manema labarai sun yi ta maimaita tambayar ta yaya aka yi irin wannna kuskure ya faru, gwamnan ya ce gwamnatinsa na yin duk abin da yakamata don tabbatar da hakan bai sake faruwa ba nan gaba.
‘Yan Hawaii sun nuna firgita lokacin da aka gargadesu da safiyar jiya Asabar, ta gidajen talabijin da radio da sakonnin email da kuma ta wayoyinsu.
Jim kadan bayan karfe takwas na safe agogon yankin, al’umomin jihar suka sami sakon dake cewa “Makami mai linzami yana kan hanyarsa zuwa Hawaii. A nemi mafaka cikin gaggawa. Wannna ba gargadin gwaji bane.”
Facebook Forum