Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump na Shirin Karawa Iran Takunkumi


Shugaba Donald Trump
Shugaba Donald Trump

Shugaban Amurka Donald Trump zai kara kakkabawa Iran wadansu sababbin takunkumi da nufin tilasawa Tehran ta daina gudanar da nazarin ayyukan makaman nukiliya, bisa ga rahotannin wadansu kamfanonin dillancin labarai da dama.

Shugaba Trump ya gana da tawagar jami’ansa na tsaron kasa kan batun Iran jiya alhamis.

Bisa ga doka, tilas ne gwamnatin Amurka ta rika tantancewa bayan kowanne kwana casa’in ko Iran tana aiki da yarjejeniyar da aka sawa hannu ta kasa da kasa a shekara ta dubu biyu da goma sha biyar ta rage ayyukanta na nukiliya ko babu. Yau Jumma’a wa’adin tantancewar yake cika.

Sai dai babbar jami’ar harkokin kasashen ketare ta KTT, Federica Mogherini tace, yarjejeniyar da aka cimma kan ayyukan nukiliya na Iran tana aiki, kuma ko da yake akwai damuwa kan rawar da Iran ke takawa a wasu kasashen gabas ta tsakiya game da ayyukan kera makaman nukiliya da wadansu ayyuka, kamata ya yi a tunkari wadannan batutuwan a wani lokaci na dabam.

Jami’ar ta bayyana haka ne bayan wani taro a Brussels jiya alhamis da ministocin harkokin kasashen ketare na kasashen Birtaniya da Faransa da Jamus da kuma Iran inda aka tattauna kan yarjejeniyar da aka cimma a shekara ta dubu biyu da goma sha biyar, da ta takaita ayyukan nukiliya na kasar Iran, inda aka ajiye cewa ita kuma Iran za’a sawwaka mata a matakan da aka kakaba mata na karya tattalinta na arziki.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG