Dalilan da suka sa Gwamnatin jihar Kano daukar matakin rufe masallacin da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ke bada sallah da gabatar da karatu su ne, "Kalaman shi na nuna kaskanci ga Annabin Rahma, Annabi Muhammdu {SA}" a cewar Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, cikin wata tattaunawa ta mussamman da Muryar Amurka.
Matakin ya biyo ne bayan wasu malamai na jihar ta Kano, da suka ja hankali akan cewar, hakan na iya haifar da hatsaniya, don haka gwamnati ta ga cewar akwai bukatar daukar matakin. Za a ga cewar kalaman ba wai kawai sun tsaya a cikin jihar ba ne, sun watsu a duniya.
Idan kuma aka lura za a ga cewar Sheikh Abduljabar, ya yi umurni da cewar kada wani ya je gidansa, har yake kwatanta irin yankan da za a yi wa duk wanda ya je gidan nasa. To kaga gwamnati ba za ta bari irin wadannan abubuwan su cigaba ba.
Kalaman nasa suna iya harzuka mutane su dauki doka a hannunsu, wannan yasa muka gaggauta daukar matakin da muka dauka. Shehin Malamin, ya roki gwamnatin ta Kano da ta ba shi damar yin mukabala da malaman jihar ta Kano, don ya kare kansa da kuma ire-iren furcinsa, wanda yake ganin cewar akan dai-dai yake.
Gwamnati ta amince da bukatar tasa, wanda suma Malaman sun yi maraba da jin hakan, inda suke bayyana cewar ai sun dade suna neman wannan damar. Gwamnatin na shiri tare da taimakon Masarautar Kano, don ganin an gudanara da wannan Muhadarar.
Yanzu haka dai ba a tsayar da ranar da za a yi wannan mukabalar ba, amma nan bada jimawa ba, za a kammala duk wasu shirye-shirye da suka kamata, za a kuma sanarwa jama'a ranar da za a yi taron, da kuma ganin an yada shirin ta kafafen talabijin da radiyo ga masu bukatar kallo da saurare.
A saurari tattaunawar Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje da Mahmud Ibrahim Kwari a cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5
Karin bayani akan: Sheikh AbdulJabbar Nasiru Kabara, Ganduje, Nigeria, da Najeriya.