Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Makiyaya A Najeriya Sun Koka A Kan Asarar Miliyoyin Dabbobi Da Suke Yi


Garken shanu a jihar Neja.
Garken shanu a jihar Neja.

Kungiyar makiyaya a Najeriya ta Miyetti Allah ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta samar da wani shirin bada taimako ga makiyayan domin rage musu radadin asarar da suke yi na dabbobin su a fadin Najeriya lamarin dake jefa su cikin kuncin rayuwa.

Sun yi kiran ne a cikin wata sanarwar bayan taro da shugabannin kungiyar ta Miyetti Allah suka yi na wuni guda tare da shugaban kwamitin amintattun kungiyar, Mai Martaba Sarkin Musulmi , Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar na biyu a Abuja.

Sanarwar bayan taron da shugaban kungiyar Muhammad Kiruwa da kuma sakataren kungiyar na kasa, Baba Othman Ngelzarma, suka sanya wa hannu na cewa, sama da shanu miliyan biyar ne aka yi asarar su ta hanyar ayyukan ‘yan bindiga da masu satar shanu da masu garkuwa da kuma batun canjin yanayi wanda yake mummunar tasiri a kan makiyayan, lamarin da ya kai su ga bukatar kayayyakin taimako.

Kasuwar Shanu a Abuja
Kasuwar Shanu a Abuja

Taron ya yi Allah wadai a kan yanda aka sace shanu da yawan su ya kai 1, 730 a karamar hukumar Kafin Koro a jihar Neja a makon da ya gabata, lamarin da ya jefa iyalai da dama cikin mawuyacin hali.

Taron ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta daukar mataki a kan wasu kungiyoyin bata gari na “Yan sakai” a jihohin Kebbi da Neja da suke zargi da kisan makiyaya 153 daga watan Maris shekarar 2020 zuwa Janairun 2021 kana an kashe kimanin mutum 30 a Bangin.

an-yi-ma-fulani-87-kisar-gilla-a-jihar-naija---miyatti-allah

ba-wanda-ya-kori-fulani-daga-jihohin-kudu-maso-yamma

gwamnan-jihar-oyo-ya-ce-ba-sa-adawa-da-fulani-makiyaya

An shirya taron da ya tattaro shugabannin kungiyar daga jihohin Najeriya 36 zuwa birnin tarayya ne domin sake nazari a kan tabarbarewar tsaro a cikin kasa da kuma yanda lamarin ya shafi mambobin kungiyar da kuma yanda ake ci gaba da alakanta dukan makiyayan da muggan ayyukan da ta’addanci a kafofin zamani da ma kafafen yada labarai.

Taron ya kuma yabawa shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF), Dr. Kayode Fayemi da gwamnonin jihohin Kebbi da Jigawa bisa kokarin daukar matakin kwantar da tarzoma biyo bayan sanarwa tashi daga jihar Ondo da aka ce an baiwa makiyaya su bar jihar.

XS
SM
MD
LG