Kakakin majalisar Dokokin Amurka John Boehner, ya sanar yau alhamis cewa zai yi murabus daga majalisa ya kuma sauka daga mukaminsa a karshen watan Oktoba.
WASHINGTON, DC —
Boehner wanda ya zama dan majalisa tun shekara ta dubu da dari tara da casa’in, yana fuskantar matsi daga jam’iyarsa ta Republican masu tsattsauran ra’ayi da aka fi sani da Tea Party kan batutuwa da dama. Yayi ta tattaunawa yau Jumma’a da nufin cimma matsaya da ‘yan jam’iyarsa da nufin kaucewa gaza gudanar da ayyukan gwamnati mako mai zuwa.
Mukamin kakakin majalisar wakilai shine na biyu a jerin wadanda zasu karbi aikin shugabancin gwamnatin Amurka idan wani dalili yasa shugaban kasa da mataimakinsa basu iya ci gaba da jan ragamar shugabancin kasar ba.
‘Yan jam’iyar Republican sun zabi Boehner a matsayin kakakin majalisa kusan shekaru biyar da suka shige ranar da ya cika shekaru 61 da haihuwa.