Da yake shiga fadar White House da Shugaba Obama, Shugaba Xi cikin raha, yace an shiga wani sabon babi a dangantaka tsakanin China da Amurka,
Shugaban Amurka yace, idan manyan kasashen nan namu muka hada hannu, zamu sauya lamura a karni mai zuwa.
Obama ya ambaci batun keta hakin bil’ama da suka zama sanadin rashin jituwa tsakanin Washington da Beijing.
Shugaba Obama yace, kasashe sun fi nasara, duniya kuma tafi ci gaba idan aka kare hakkokin bil’adama.
Xi ya iso Washington yau alhamis rana ta biyu ta ziyarar aikin mako guda da ya kawo nan Amurka da ya fara yada zango a Seattle, inda shugaban kasar Chinan
yaba kamfanonin Amurka tabbacin cewa, yana kokarin samar da kyakkyawan yanayin zuba jari a kasarsa.
Da yamma kuma shugaba Obama zai karbi bakuncin takwaransa Xi a wata karamar walimar cin abincin dare. Mataimakan shugabannin sunce tattaunawar da zasu yi a kadaice, ita ce dama ta farko da zasu fara tattaunawa kan muhimman batutuwa yayin ziyarar Xi ta mako guda.