Kaduna:Takaddamar Mukamin Kakakin Majalisa

  • Ibrahim Garba

Janar Muhammadu Buhari a Gombe Fabrairu 3, 2015.

Yayin da ake dosar lokacin mika mulki ga gwamnati mai jiran gado, a jihar Kaduna an shiga gardama kan inda Kakakin Majalisar Dokokin jihar zai fito.

An shiga takaddama kan mukamin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna tsakanin shiyya ta daya da ta biyu.

Yayin da shiyya ta biyu ke cewa zababben gwamnan hijar dan shiyya ta daya ne don haka ya kamata Kakakin Majalisar Jihar ya fito daga shiyya ta biyu, ita kuma shiyya ta daya cewa ta ke ai zababben gwamnan dan shiyyar ta biyu ne shi; don haka kamata ya yi kakakin majalisar dokokin ya fito daga shiyya ta daya.

Wannan takaddamar ta sa wakilin Muryar Amurka a kaduna Isah Lawal Ikara, ya tuntubi zababben gwamnan, Malam Nasiru el-Rufa’i, don inda ya fito. El-Rufa’i dai ya ce shi haifaffen Zariya ne, to amma ya na daukar kansa a matsayin dan shiyya ta biyu saboda a nan ya girma kuma anan yak e da cikakken gida kuma anan ya yi aiki.

Hasalima tun ya na dan shekaru takwas da haihuwa aka kai shi unguwar Kawo kaduna, inda ya girma. Ya ce bayan ya kammala makaranta ya zauna a Zariya inda ya yi aiki amma duk bai wuce na tsawon wata shida ba.

Zababben gwamnan ya ce ‘ward’ din da ya yi rajista na Unguwar Sarki ne. El-Rufa’I ya kara da cewa, “saboda haka, a wannan tafiya a siyasance ni dan Zone Two ne, kodayake asalina ni dan Zone One ne.”

Da Isah ya tambaye shi yadda za a raba mukamai a jihar a gwamnatinsa kuwa, sai El-Rufa’i ya ce bai kamata mutane su ba da muhimmanci ma tsarin ware mukami wa wani takamaiman bangare ba, abin da ya kamata a mai da hankali akai shi ne ingancin mutum.

“Mu a gwamnatinmu ba za mu ce wai za mu raba mukami a ba ma wannan na nan ba, a ba da wannan na can ba; duk lokacin da mukami ya fito ya za dubi mutum ne wanda ya cancanta – idan kuma mutane 10 daga wuri daya su ke – in za su yi wa mutanen jiha aiki, za mu sa su domin jihar Kaduna day ace.”

Haka zalika, da Isah ya tambayi mataimakin gwamnan jihar mai jiran gado, Honorabul Barnabas Bala Bantext y ace bisa ga kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC, bubu tsarin ware mukami ga takamaimun bangarori.

Isah Lawal Ikarah ya lura cewa har yanzu al’ummar jihar ta Kaduna na tambayar bangarorin da Kakakin Majalisar Dokokin jihar da kuma Ministan da zai wakilci jihar za su fito.

Your browser doesn’t support HTML5

Kaduna:Takaddamar Mukamin Kakakin Majalisa - 3'52''