Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Goodluck Jonathan Yayi Taron Majilisar Kasa na Karshe


Taron Majalisar Kasa
Taron Majalisar Kasa

Shugaban kasar Najeriya Goodluck Ebelle Jonathan yayi taron majilisar kasa na karshe na jamhuriya ta bakwai karkashin jagoran sa, tare da halartan dukkan tsoffin shugabannin kasa,tsofaffin shugabannin bangaren Sharaa dana majilisar kasa da kuma gwamnoni, da manyan mukarabbai masu bada shawara a gwamnati.

A wurin taron an tattauna abinda ya shafi zaben da ya gabata da kuma matsaloli na tsaro da tattalin arziki da sauran abubuwan da ake ganin cewa kasa na bukata domin ci gaba da kyautata rayuwar al’umma.

Bayan da aka kammala taron na kasa Gwamnan jihar Niger Dr Muazu Babangida Aliyu yayi wa manema labarai bayani akan sakamakon irin abubuwan da aka tattauna kamar haka.

‘’Na daya mun nuna farin cikin mu ga yadda zabe ya gudana, da kuma yada wadanda zaben ya shafa musammam yadda suka riko abin, da yadda suka tafiyar da sakamakon zabe.Na daya muka yabi shi shugaban kasa, duk da yake yasha kaye, ya yadda yasha kaye dai-dai da kuma shi wanda aka zaba wanda zai karbi hannun shugaban kasa ranar 29 cewa shima wanda yayi duk da cewa yayi nasara bai nuna cewa akwai wata gayya a ciki ba wannan ya taimaka muna kwarai da ya kawo zaman lafiya kwarai a kasar mu, kuma abinda muke so ayi koyi dashi Kenan ako ina.Na biyu muka dubi batun mika hannu da yadda aka shirya shi da kuma yadda yakamata a dunga shiri domin da can kowanne yakan yi nashi ne, amma yanzu muna so ne ko yaushe idan mika hannu to haka za ayi, mun shirya cewa ranar jumaa za ayi adduoi a masallatai, ranar lahadi ayi a coci-coci, ranar 28 za a bada takardu, ranar 29 za a rantsad da shugaban kasa mai jiran gado, sai kuma mukayi maganar zaman tsaro a Najeriya baki daya, muka dubi abinda ke faruwa na boko haram da irin nasarori da aka yi da kuma irin fadace-fadace na wurare da yawa da sauran su, akwai maganganun da ya shafi tsaron kuma amma su bana nan kansul din bane, sai muka ce to a koma Economic Council a dubi wadannan kamar su batun Petrol da batun harajin kasa da sauran su.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:58 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG