Kada Kungiyar Kwallon Kafar Paris Saint-German Tayi Dogaro da Ibrahimovic.

Kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint-German ba zata dogara ga Ibrahimovic ba domin samun nasarar ta.

Tsohon dan wasan nan na kungiyar kwallon kafa na Paris Saint Germain Jay-Jay Okocha, yace kungiyar ba zata ce zata dogara ga Zlatan Ibrahimovic, na tayi nasara a wasan ta na rukuni-rukuni

Jay jay Okocha ya bayyana cewa kamata yayi kungiyar ta kara samun mutane a kalla 3 ko 4 domin ta samu kwarin gwiwar cin kofin wasan kungiya-kungiya na kasashen turai

Ba shakka Ibrahimovic, shine ya zura kwallaye 3-1 a wasan su da kungiyar Ajax wanda suka yi ranar talatar data gabata, amma duk da haka Jay-Jay Okocha yace wannan ba hujja bace, shi dai Okocha yayi wasa a kungiyar Parc de Paris a tsakanin shekarar alif dari tara da 98 da kuma shekara ta 2002.

Okocha ya shaidawa wa mujallar goal cewa, “a halin yanzu Ibrahimovic shine zakaran su a kungiyar amma ana bukatar mutane 3 zuwa 4 domin samun tabbacin cin wannan gasar

Yaci gaba da cewa idan aka dogara ga dan wasa guda domin samun nasara to idan yazo wasan taki shi fa? Ko kuma ya samu rauni to sai yaya, don haka bai da kyau ace an dogara ga dan wasa guda, sai dai Okocha yace yana da kwarin gwiwa cewa wata kungiyar ta PSG zata samu nasarar daukar wannan kofin.

Your browser doesn’t support HTML5

Labarin Wasanni - 1'00"