Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Cire Najeriya Daga Gasar Cin Kofin Kwallon Kafa Na Kasashen Afirka


'Yan wasan Super Eagles na Najeriya
'Yan wasan Super Eagles na Najeriya

Karshenta dai, Najeriya ba zata samu damar kare kofin zakarun kasashen Afirka dake hannunta ba, a bayan da aka yi waje-rod da ita jiya laraba.

Kasashen Kwango, da Kwnago ta Kinshasa, da Ghana da Guinea, da Ivory Coast da kuma Mali duk sun samu tsallakewa suka hadu da kiasashe 10 da su kam tuni suka haye zuwa wannan gasa da za a yi a kasar Equatorial Guinea.

Najeriya tana bukatar ta doke Afirka ta Kudu dake saman rukuninsu a sabon filin wasa na Uyo, domin hayewa zuwa gasar. Amma kash, da kyar Najeriya ta samu aka tashi kunnen doki, bayan da 'yan Bafana Bafana suka yi gaba da kwallaye biyu.

Kasar Kwango ta zamo ta biyu a bayan Afirka ta Kudu a lokacin da ta doke Sudan da ci 1 da babu, ta kasance tana da maki 10, Najeriya tana da 7.

A watan da ya shige, Aljeriya da Cape Verde suka samu hayewa a bayan wasanni 4 kacal, sannan a karshen makon da ya shige Burkina Faso da Kamaru da Gabon da Senegal da ATK da Tunisiya da kuma Zambiya suka bi sahunsu.

XS
SM
MD
LG