Kabilun Fulani, Kuteb Da Tiv Na Jihar Taraba Sun Sa Hannu Kan Wata Yarjejeniyar Zaman Lafiya

Kabilun Fulani, Kuteb Da Tiv Na Jihar Taraba Sun Sa Hannu Kan Wata Yarjejeniyar Zaman Lafiya

Ana fatan wannan sa hannu da kabilun suka yi zai kawo karshen dukkanin wani rikici a yankin Takum da wasu yankunan da ke faam da rikici.

TARABA, NIGERIA - Taron tattaunawan an kwashe tsawon wata guda ana neman mafita domin cimma matsaya kamar dai yadda shugaban kwamitin sulhu Reverend Recen Yakubu ya fada bayan sun kammala taron a karamar hukumar Takum.

Kabilun Fulani, Kuteb Da Tiv Na Jihar Taraba Sun Sa Hannu Kan Wata Yarjejeniyar Zaman Lafiya

Kabilun Fulani, Kuteb Da Tiv Na Jihar Taraba Sun Sa Hannu Kan Wata Yarjejeniyar Zaman Lafiya

Ya’u Ibrahim Barewa mataimakin shugaban kungiyar tabital pulako junde jam a Jihar Taraba ya ce wannan sa hannu da suka yi zai kawo karshen dukkanin wani rikici a yankin na Takum da wasu yankuna gaba daya.

Shugaban karamar hukumar USSA Hon. Abrshi Musa Bala, ya tabbatar da cewa shi ma ya gamsu da yadda aka gudanar da wannan zaman na sulhu da aka kwashe wata guda ana gudanarwa.

Kabilun Fulani, Kuteb Da Tiv Na Jihar Taraba Sun Sa Hannu Kan Wata Yarjejeniyar Zaman Lafiya

Ya kara da cewa za a samu zaman lafiya mai dorewa a yankunan kananan hukumomin da lamarin ya shafa a Jihar Taraba.

Saurari cikakken rahoto daga Lado Salisu Muhammad Garba:

Your browser doesn’t support HTML5

Kabilun Fulani, Kuteb Da Tiv Na Jihar Taraba Sun Sa Hannu Kan Wata Yarjejeniyar Zaman Lafiya .mp3