Kabilun Arewacin Najeriya Sama Da 300 Sun Gana A Jos

Hoto da aka dauka bayan farmaki kan Majami'ar COCIN A Jos.

Hoto da aka dauka bayan farmaki kan Majami'ar COCIN A Jos.

A jiya Asabar ne kabilu sama da 300 daga Arewacin Najeriya, sun gudanar da wani taro a birnin Jos dake Jihar Filato domin tattauna matakan shawo kan matsalolin tsaro da yankin na Arewacin Najeriya yake fuskanta.
Ganin yadda yankin Arewacin Najeriya ya fada cikin tashe-tashen hankula da kashe-kashe, lamarin da yasa al-ummar arewa ke zaune cikin talauci da zulumi, wannan shine yasa kabilu daga yankin na Arewa suka shirya wani taron fadakar da juna akan yadda zasu inganta zamanta kewar su da abokan zaman su da kuma bada shawarwari wa Gwamnati, ta yadda za’a samu fahimtar juna tsakanin al-ummomi dake yankin na Arewa.

Wakiliyar Muryar Amurka a birnin Jos, Zainab Babaji ta gana da Mr. Mark Libdo, shugaban kungiyar Stefanos Foundation, kungiya mai neman ‘yancin Krista a Arewacin Najeriya.

“Abubuwan dake faruwa a Arewacin Najeriya ba sabon abu ne yanzu, kashe-kashen da akeyi ya shafi kowa, kuma kabilun sun duba yadda ya shafe su, shine suka ce ya kamata a hada kai, domin a duba yadda za’a dauki matakai na rayuwa a arewa.” Kalaman Mr. Mark Libdo kennan.

Fasto Chris Bature shine ko’ordinaton kungiyar Bishara ta al-ummar Birom.

“Babban abun shine cewa gwamnati tilas ta gane cewa dole ta zama gwamnatin gaskiya. Gwamnati tilas ta sani gwamnati na kowa ne, ko kabilarka na mutane goma ne, in dai kana Najeriya, kaima kana da ‘yanci. Don haka gwamnati ta kyale mutane domin kowa ya samu.” A cewar Fasto Chris Bature.

Kimanin kabilu fiye da 300 daga jihohi goma sha uku ne suka hallarci taron.

Your browser doesn’t support HTML5

Taron Kabilu Sama Da 300 Daga Arewacin Najeriya - 2:54