Joe Biden Ya Damka Wa Mata Sashen Sadarwa Na Fadar White House

Zababben shugaban Amurka Joe Biden

Zababben shugaban Amurka, Joe Biden da Mataimakiyar Shugaban mai jiran gado Kamala Harris, sun sanar da nadin tawagar mata zalla a fannin sadarwa.

"Sadarwa kai tsaye ta gaskiya ga jama'ar Amurka na daya daga cikin mahimman ayyukan shugaban kasa, kuma za a damka wa wannan tawaga babban nauyin hada Amurkawa da Fadar White House," a cewar Biden cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai. daga ofishin kwamitin karbar mulki.

Ya kara da cewa "Wadannan kwararrun masana sadarwa suna kawo ra'ayoyi daban-daban ga aikinsu da kuma sadaukar da kai, don gina kasar nan da kyau."

Kate Bedingfield, wacce ta yi aiki a matsayin darektar sadarwa na yakin neman zaben Biden-Harris, an nada ta daraktar sadarwa ta Fadar White House.

Ita kuma, Pili Tobar, wacce ta yi aiki a matsayin mataimakiyar darakta a kungiyar Muryar Amurkawa, wata kungiya mai rajin kawo sauyi kan shige da fice, za ta zama mataimakiyarta.

Sai kuma, Ashley Etienne, wacce ta yi aiki a matsayin darektar sadarwa ta Kakakin Majalisa Nancy Pelosi, an nada ta a matsayin daraktar sadarwa ta Harris.