Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Biden Na Shirin Gabatar Da Jami'an Da Zai Nada a Gwamnatinsa


Joe Biden
Joe Biden

Zababben shugaban Amurka Joe Biden zai yi wani taro a yau Talata domin gabatar da mutanen da yake so ya zaba don rike manyan mukamai na diplomasiyya da na tsaron kasa a gwamnatinsa.

Daga cikinsu a akwai Antony Blinken, daya daga cikin makusantan Biden a tsakanin masu ba shi shawara kan harkokin kasashen waje – wanda shi ake sa ran zai rike mukamin Sakataren Harkokin wajen Amurka.

Biden ya kuma ce yana da niyyar daukan tsohon sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry domin rike sabon mukamin wakilin shugaban kasa na musamman kan yanayi, yayin da zai kuma rike wani mukami a Majalisar tsaron Kasa.

Hakan, mataki ne da ke nuna yadda shugaban mai jiran-gado zai mayar da hankali kan yadda za a tunkari batun sauyin yanayi a matsayin batu na gaggawa a cewar tawagar karbar mulkin Biden.

Wannan na faruwa ne yayin da hukumar da ke kula da ayyukan tafiyar da mulki a nan Amurka, ta amince cewa Biden ya cancanci a ba shi duk hadin kan da yake bukata bisa tanadin da dokar 1964 ta yi, don a samu damar mika mulki ba tare da wata tangarda ba.

A tsakanin yanzu zuwa ranar 20 ga watan Janairu da za a rantsar da shi, Biden zai ci gaba da nade-naden mukamai a gwamnatinsa na jami’an da za su aiwatar da manufofinsa, idan ya karbi ragamar mulki – ya kuma samu damar tafiyar da fannin tsaron kasa.

Tuni tawagarsa ta karbar mulki ta samu damar shiga shafin yanar gizon gwamnati inda har ta kirkiri wani shafi mai taken buildbackbetter.gov. da ke nufin kyautata al’amuran kasar.

Biden zai kuma samu bayanai kan yanayin barazana ga tsaron kasa, ayyukan soji na boye da wasu matakan da gwamnatin Trump ke shirin aiwatarwa ta fuskar soji.

Hakazalika gwamnatin Trump za ta yi wani taro da ma’aikatan Biden don bitar abin da ya shafi zama cikin shirin kar-ta-kwana.

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG