Iran tayi watsi da bukatar Amurka ta neman maida mata jirgin saman ayyukan leken asirin da babu matuki a cikinsa. Jirgin saman da Iran tace ta kakkabo daga sama a kusa da kan iyakar kasar da Afghanistan a farkon wannan watan.
A Talatar da ta gabata ce aka ji mukadashin Ministan tsaron Iran, Janaral Ahmad Vahidi, yana cewa yanzu wannan jirgin saman yakin ya zama mallakin kasar Iran.
Haka kuma anji gidan rediyon kasar Iran yana ambaton mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, Ramin Mehmanparast, yana fadin cewa tura wannan jirgin saman leken asirin da Amirka tayi, keta ka’idar matakan tsaron kasar ne don haka kamata yayi Amirka ta nemi gafara.
Yace ya kamata, Amirka ta san cewa matakin da ta dauka keta ka’idar sararin samaniyar Iran ne, kuma yana iya janyo barazana ga matakan tsaro da zaman lafiya a duniya.