Jirgin Kasan Kaduna Zuwa Abuja Ya Kauce Hanya

Yadda kan jirgin ya kauce hanya (Hoto: Facebook/Freedom Radio FM)

Wannan al’amari ya faru ne mako guda bayan da wani jirgin kasan na Najeriya ya kauce hanya a jihar Kogi yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa  Warri daga Itakpe.

Wani jirgin kasan da ya taso daga Kaduna zuwa Abuja ya yi hatsari a yankin Kubwa da ke Abuja, babban birnin Najeriya.

Lamarin ya faru da tsakar ranar Juma’a sa’ilin da jirgin ya kusa kai wa tashar da zai tsaya a Abuja.

Bayanai sun yi nuni da cewa kan jirgin ya kaucewa hanya ya kuma jirkice gefe guda.

Babu wani rahoto da ya nuna cewa an jikkata a hatsarin.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Babban Darektar hukumar sufurin jirgin kasa ta NRC a Najeriya Injiniya Fidet Okhiria ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Sai dai bai fadada bayanansa ba domin ya ce suna kan tattara bayanai kan abin da ya faru.

Wata fasinja da ke cikin jirgin ta fadawa gidan rediyon Freedom FM da ke Kano cewa, fasinja da dama sun taka da kafa domin isa inda za su sauka.

Wannan al’amari ya faru ne mako guda bayan da wani jirgin kasan na Najeriya ya kauce hanya a jihar Kogi yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Warri daga Itakpe.

Hukumar ta NRC ta ce tuni an dukufa wajen gudanar da gyare-gyare bayan wannan hatsari da ya auku.