Wannan harin na daga cikin jerin hare-hare a baya-baya nan da ake kai wa a sassan Najeriya, lamarin da ya zama wani babban kalubale ga gwamnatin kasar gabanin zaben shugaban kasa da ke tafe a watan Fabrairu.
A wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan jihar ta fitar, ta ce wasu 'yan bindiga da ake kyautata zato makiyaya ne, dauke da makamai suka kai harin a tashar jirgin kasan Tom Ikimi mai tazarar kilomita 111 da Benin babban birnin jihar kuma kusa da kan iyaka da jihar Anambra da misalin karfe 4 na yamma, yayin da fasinjoji ke jiran jirgin kasa zuwa birnin Warri na jihar Delta, a cewar kamfanin dillancin labaran Reuters.
‘Yan sandan sun ce an harbe wasu mutane a tashar a lokacin harin.
Kwamishinan yada labarai na jihar Edo, Chris Osa Nehikhare, ya ce maharan sun yi garkuwa da mutane 32, ko da yake daya daga cikin su ya tsere.
“A yanzu haka jami’an tsaro da suka hada da sojoji, da ‘yan sanda, da ‘kungiyar ‘yan banga, da kuma mafarauta, suna ci gaba da gudanar da bincike da yin duk abinda ya dace don kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su,” inji Nehikhare.
Ya kara da cewa, muna da kwarin gwiwa za a ceto sauran wadanda harin ya rutsa da su nan da sa'o'i masu zuwa."
Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta Najeriya (NRC) ta rufe tashar zuwa wani lokaci, a cewar Reuters.
A watan da ya gabata ne hukumar NRC ta sake bude layin dogo da ya hada babban birnin tarayya Abuja da jihar Kaduna a arewacin kasar, watanni bayan da wasu ‘yan bindiga suka fasa titin jirgin kasan, suka yi garkuwa da fasinjoji da dama tare da kashe mutane shida. Sai a karshen watan Oktoban shekarar 2022 aka kubutar da sauran wadanda aka yi garkuwa da su a harin da aka kai a watan Maris.