Jirgin Falcon 9 Da Na'urar Hangen Taurari Sun Raba Gari

A jiya Laraba ne jirgin Falcon 9, dauke da sabon jirgin SpaceX na hukumar binciken sararrin samaniya ta Amurka NASA, ya tarwatse a cikin duniyar wata, lokacin da yake kokarin shiga duniyar, inda na’urar hangen nesa zata kidaya yawan taurarin da ake dasu a duniyar ta wata.

An dakatar da tafiyar jirgin zuwa duniyar har na kwanaki biyu, wanda aka harba shi daga sansanin sojojin sama na kasar Amurka dake jihar Florida, da misalin 6:51 na yamma. Wanda ake sa ran na’urar zata rika lura da yadda duniya ke juyawa, da adadin taurari da suke kai kawo a kowace shekara.

Duk dai da cewar babbar na’urar ta tsallake rijiya da baya, inda ta tsinke daga jirgin na Falcon 9, ta nemi hanyar dawowa wannan duniyar batare da matuki ba, ta sauka a kan wani jirgin ruwa dake yawo cikin tekun Atlantic, ba’a sanar da sunan jirgin da ta sauka akan shiba zuwa yanzu.

Ana sa ran bangaren da ya sauka cikin tekun, za’a iya amfani dashi a zagaye na biyu, don kara tura shi cikin sararrin samaniya, da zummar gudanar da aikin da ake kokarin cinma na irga yawan taurari da ke yawo a duniyar wata a kowace shekara.