Wani mai magana da yawun gidajen kason jihar South Carolina mai suna Jeff Taillon ya ce fursunoni 7 sun mutu wasu su 17 kuma sun raunana, akan dole aka kai su waje don jinyarsu bayan sa’o’in da aka kwashe ana fada a cikin wani gidan kaso dake da tsauraran matakan tsaro.
Mr. Jeff Taillon ne ya sanar da sakamakon mummunan fadan da ya faru bayan da jami’an tsaron yankin suka taimaka wajen kwantar da fitinar a gidan kason dake karamar hukumar Lee, da karfe 3 na safiyar Litinin.
Taillon ya ce babu jami’in tsaron da ya jikkata bayan da fadan ya barke da karfe 7:15 na yammacin Lahadi.
Jami’an kwana-kwana da agaji dake garin Lee sun ce motocin jinya dayawa sun je gidan kason don kulawa da wadanda suka jikkata.
Gidan kason Bishopville, mai cike da tsauraran matakan tsaro na dauke da fursunoni 1,500, ciki harda mugaye, da dadaddun masu laifin jihar South carolina. An taba cakawa wasu jami’an tsaro su 2 wuka a wani fada da aka yi a shekarar 2015. Ko a watan Fabarairu ma sai da aka kashe wani fursuna a wurin.
Facebook Forum