Kasar Australia nada nau’ukan kwadi kimanin sama da 240, harda wasu launuka da babu irin su a ko ina a fadin duniya, wasu daga cikin nau’ukan kwadin suna raguwa a doron kasa, musamman launin kwadi masu ratsin tsanwa da kore.
Hakan yasa hukumomi a kasar tashi tsaye wajen gano musabbabin abkuwar hakan, wanda a shekarar da ta gabata ne aka kirkiri wata manhaja don kidayar kwadin, da kuma sanin adadin nau’uka da suka rage.
Ya zuwa yanzu al’ummah a kasar sun bada goyon baya wajen saukar da manhajar, da aka kirkira don kidayar a wayoyin su na zamani, a yanzu an samu kimanin adadin kwadi da suka kai yawan 18,663 an kuma tantance adadin 22,504 kana an samu karin nau’uka 141.
Manhajar ta taimaka matuka wajen gano wasu nau’uka da babu su acikin kundin bayanan adadin kwadi da ake dasu a kasar, kamar kwado mai suna “Cane Toad” kana da tantance wurare da kwadi ke samun nishadi, da jin dadin zama, haka da sanin inda basa sha’awar zama.
Binciken ya kara bayyana irin yanayi da kwadi ke samun walwala, kana da kara fahimtar kowane nau’in kwado da irin yanayin da yake mishi dadi, kodai lokacin hunturu ko na kaka, da bazara.
Kimanin mutane ashirin da suka shiga cikin kidayar, sun bayyana kaso mafi yawa na yawan kwadin da aka kidaya a baki dayan kasar, inda aka samu mutun daya ya dauki hotunan nau’ukan kwadi 469, sai wanda ya dauki hotunan mafi karanci na kwadi 29.
Binciken yanayi a fadin duniya ya tabbatar da cewar, yankuna masu yawan kwadi, na daga cikin yankuna masu lafiyayyen wurin rayuwa ga ‘yan’adam, duk inda kwadi ke rayuwa, babu shakka za’a samu iska mai nagarta ga lafiya bi’adama.
Facebook Forum