Rahoton wani bincike da aka fitar wanda yake bayyana wasu illolin da amfani da namun daji don Nishadantar da yara, kan iya haifarwa ga rayuwar yau da kullun, binciken ya bayyana cewar hakan zai canza tunanin mutane.
A inda hakan zai iya saka rayuwar yara cikin rudani, domin kuwa yara suna daukar wadannan dobbobin abin so, ganin yadda suke fitowa a fina finai a matsayin abin sha’awa da kuma nuna kauna. Da yawa namun dajin akan nuna su a matsayin abokan yara.
Kwakwalwar yara bata ganin dabbobin a matsayin wasu halittu da ka iya cutar da rayuwar su, sau da yawa akan yi fina finai da ake nuna namun daji kamar su damisoshi, zakoki, kuraye, giwaye, da dabbar biya.
Marubucin ya kira wannan binciken da suna “Rayuwar tare, batare da banbanci tsakanin hallitar mutun da ta namun daji” ganin yadda ake kera kayan wasan yara na namun daji, don kuwa ko a shekarar 2010 an sayar da ‘yar-tsanar Sophie a kasar Faransa da suka nunka yawan baki daya rakumin dawan dake kasashen Afrika.
Marubucin ya baiwa kamfanonin da suke kera kayan wasa masu jinsin namun daji da su dinga bada kudaden shigarsu ga hukumomi masu kula da namun daji.
Facebook Forum