Jihar Taraba Ta Fito Da Wani Sabon Salon Rigakafin Kwayar Cutar Polio

Rigakafin Cutar Polio

Gwamnatin jihar Taraba ta kaddamar da wani shiri na yin amfani da shingayen da sojoji ke bincikar motoci domin gudanar da rigakafin cutar shan‘inna ko Polio ga kananan yara.

A cewar gwamnatin jihar wannan wani yunkuri ne na tabbatar da cewa an yiwa dukkannin yara dake jihar rigakafin. Tun bayan sake bullowar cutar a kananan hukumomin Gwoza da Jere na jihar Borno, sauran jihohi dake Arewa maso Gabashin Najeriya suka tashi tsaye domin daukar matakin kariya daga yaduwar kwayar cutar.

Wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdul’aziz, ya ziyarci ‘daya daga cikin manyan shingayen da sojoji ke bincikar mutane kafin shiga garin Jalingo ko kuma fita daga garin, inda ya iske wata tawagar jami’an lafiya wanda da dukkan alamu suna gurin ne domin gudanar da aikin rigakafi a shingen.

Daya daga cikin ma’aikatan lafiyar ya shaidawa Ibrahim cewa, suna samun hadin kan matafiya wajen gudanar da aikinsu wanda suke duba hannun yara don tabbatar da cewa an yi musu rigakafin, duk da yake wasu kan bar gidajensu kafin karasowar ma’aikatan lafiya.

Sake bullar wannan kwayar cutar polio a jihar Borno a watan jiya na Agusta, yazo ne a dai dai lokacin da ake haramar saka Najeriya a cikin jerin kasashen da suka yi bankwana da cutar Shan’inna.

Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Ibrahim Abdul’aziz.

Your browser doesn’t support HTML5

Jihar Taraba Ta Fito Da Wani Sabon Salon Rigakafin Kwayar Cutar Polio - 2'52"