Jihar Maine da ke Amurka ta cire sunan Trump a zaben fidda gwani da za a yi a jihar.
A makon da ya gabata jihar Colorado ta dauki irin wannan mataki na hana tsohon shugaban na Amurka wanda ke neman tsayawa takara a zaben da za a yi badi.
Sakatariya Shenna Bellows, ta kasance jami’ar zabe da ta dauki wannan mataki na hana Trump karkashin dokar ta 14.
A lokacin yakin basasan da aka yi a Amurka aka samar da dokar wacce ta hana wadanda suka yaki gwamnatin Amurka rike wani mukamin gwamnati.
Shi dai Trump ya fada karkashin wannan doka ne saboda samunsa da hannu a harin da aka kai ginin Majalisar Dokokin Amurka a ranar 6 ga watan Janairun 2021.
Ita ma jihar Colorado wannan doka ta yi amfani da ita wajen hana Trump din shiga zaben.
Kotun Kolin Amurka za ta duba wannan batu, inda za ta fayyace ko dokar ta shafi Trump kuma ko zai iya tsayawa takarar shugaban kasa.
Shi dai Trump ya sha musanta hannu a harin da aka kai ginin majalisar.