Jihar Kaduna na Gap da Samun Sabbin Kwamishanoni

Aikin noma a Kaduna

Kwanakin baya ne gwamnan Kaduna ya rushe majalisar zastarwar jihar daga bisani kuma ya mika wa majalisar dokokin jihar sunayen wadanda yake son ya nada.
Bisa ga alamu ba da dadewa ba gwamnan jihar Kaduna na iya rantsar da sabbin kwamishanoni domin su kama aiki gadan-gadan.

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta kammala tantance sunayen da gwamna Mukhtari Ramalan ya mika mata da ya ke so ya nada sabbin kwamishanoni domin su maye gurbin wadanda ya saukar. Jadawalin sunaye ashirin da hudu ya nuna cewa kowace karamar hukuma ta samu kwamishana daya sai dai karamar hukumar Zango Kataf dake da biyu.

Dan majalisa Yakubu Yusuf Soja shugaban yada labaru na majalisar ya sanarda hakan inda ya ce majalisar ta yi zama ranar Laraba da Alhamis ta kuma tantance sunaye ashirin da hudu da gwamnan ya mika mata. Cikin sunayen akwai mata biyu. Ya ce wannan shi ne karo na farko da basu sami korafe-korafe ba kan kowane suna cikin ashirin da hudun domin dukansu 'yan siyasa ne. Lokacin tantancewa babu wata tangarda ko matsala da suka samu domin dukansu sun amsa tambayoyin da aka yi masu a natse.

Daga karshe ya bukaci mutanen Kaduna su taimaki majalisar da addu'a domin ta cigaba da yin aikinta bisa ga ikon da kundin tsarin mulkin kasa ya bata. Ya ce suna da bukata su yi aiki tare da yin adalci. Yana fata kuma jihar zata cigaba da zama cikin lafiya.

Isah Lawal Ikara nada rahoto.

Your browser doesn’t support HTML5

Jihar Kaduna Na Gap Da Samun Sabbin Kwamishanoni - 2:44