Dr Nazeef ya zubar da hawaye yayin da hukumar SSS ta gabatar da shi tare da wasu mutane biyar a gaban kotu da hukumar ta ce abokan burminsa ne. Babban lauya Hassan Liman na daya daga cikin lauyoyin dake kareshi. Ya ce da suka kamashi kusan wata daya kenan babu wanda ya san inda yake. Kawoshi kotun ya sa aka san inda yake yanzu. Zargin da jami'an tsaro suka yi na cewa an sami Dr. Nazeef da makamai ba gaskiya ba ne kuma su kansu jami'an tsaron sun san da hakan. Lauyan ya ce sun riga sun lissafa duk abun da suka ce sun gano.
Kungiya Izala ta nemi kotu ta saki Dr Nazeef ba tare da bata wani lokaci ba.Kungiyar ta ce bashi da alaka da kungiyar ta'adanci balantana kuma ta'adanci. Sheikh Bala Lau shi ne shugaban kungiyar ta kasa. Ya ce Dr Nazeef malamin sunna ne babu ruwansa da ta'adanci. Ya ce idan sun yi shiru basu yi magana ba to kenan za'a cigaba da kama malaman sunna ba gaira ba dalili ana kulle su ana cin zarafinsu. Idan sun yi shiru basu dauki mataki ba to Allah kadai ya san abun da zai faru nan gaba. Don haka kungiyar na kira a sakeshi. Malami ne na sunna wanda bashi da alaka da kungiyar ta'adanci. Idan akwai wadanda suke koyas da mutane cewa akidu irin na su Boko Haram ba daidai ba ne Dr Nazeef yana ciki. Kamashi da daureshi da aka yi ba'a yi masa adalci ba. Ya ce irin wannan yake haifar ma kasa da al'umma tashin hankali da fitina.
Nasiru Adamu El-Hikaya nada karin bayani.