Wadannan na cikin shawarwarin da kwamitin bincike da ta nada kan kisan da aka yiwa matasa a Apo, Abuja da ta amince da su. Majalisar ta kafa kwamitin ne domin bincikar abun da ya kaiga kashe matasan a lokacin da jami'an tsaro suka kai samame. Kwamitin wanda Janaral Mohammed Magoro mai ritaya ya jagoranta ya jaddada bukatar gwamnatin tarayya ta kirkiro wasu sabbin dabaru wajen shawo kan tashin hankula a kasar.
Bayan majalisar ta kwashi sa'o'i tana muhawara kan rahoton wanda ya samu sa hannun sanatoci 20, Sanato Sahabi Yau daga jihar Zamfara wanda ya rasa wani daga mazabarsa ya ce nai gamsu da rahoton ba domin yawancin abun da aka ce kwamitin ya yi bai yi ba. Ya ce an nemi kwamitin ya binciko ko su matasan da aka kashe 'yan kungiyar Boko Haram.
Kamar ita majalisar dattawa majalisar wakilai tana nata binciken kamar yadda wani dan majalisar Ahmed Tukur Idris ya tabbatar. Ya ce kawo yanzu jami'an tsaro sun saki hudu daga cikin wadanda aka kama da yi masu kashedin kada su dawo cikin birnin Abuja har na tsawon shekaru uku.
Medina Dauda nada karin bayani