Shugaba Tinubu ya fara ne da yin tsokaci kan batun tallafin man fetur da ake ta cece-kuce akan sa a kasar, inda ya jaddada cewa cire shi wani mataki ne da ya dace don tunkarar kalubalen tattalin arzikin da Najeriya ke fuskanta.
Ya kara da cewa tallafin ya janyowa kasar asarar tiriliyoyin naira a duk shekara, wanda kamata yayi ace an yi amfani da su wajen ayyukan kyautata rayuwar jama’a kamar su sufuri, kiwon lafiya, ilimi, da kuma tsaron kasa.
A maimakon haka, ya ce, an fitar da kudaden ne domin cin gajiyar wasu gungun masu hannu da shuni kalilan, lamarin da ke barazana ga daidaiton tattalin arzikin kasar da kuma dimokradiyya.
Shugaban ya bayyana kudirinsa na sake fasalin tattalin arziki da yaki da manyan matsalolin da suka dade suna addabar al’ummar kasar. Ya kare matakin kawo karshen tallafin man fetur da tsarin musayar kudaden musayar kudi, yana mai bayyana muhimmancinsu wajen gina tattalin arziki mai inganci da dakile tasirin wasu tsirarun mutane masu hanu da shuni wadanda basa wakiltar kowa sai kansu.
Shugaba Tinubu ya amince cewa tsarin gyaran na iya haifar da wahalhalu da rashin tabbas ga ‘yan kasa amma ya tabbatar musu da cewa ya zama dole domin amfanin al’umma na dindindin.
Don rage nauyin wahalhalun tattalin arziki a kan 'yan kasuwa da ma'aikata, shugaba Tinubu ya sanar da matakai da dama, inda ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na aiki tare da hadin gwiwa da gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi don aiwatar da wasu muhimman tsare-tsare da nufin dakile tasirin yanayin wahala da radadi sakamakon matakan da aka dauka akan tattalin arziki ga al’ummar kasar ta Najeriya.
Tun a farko farkon watan Yulin wannan shekara ne shugaba Tinubu ya sanya hannu kan wasu dokokin shugaban kasa guda hudu don magance manufofin kasafin kuɗi maras aminci da haraji da yawa da ke kawo cikas a harkokin kasuwanci.
Waɗannan dokokin in nji shi, suna da mahimmanci musamman ga masana'antu don bunƙasa su da samar da ayyukan yi.
Bugu da kari, shugaba Tinubu ya bayyana shirinsa na zuba jarin naira biliyan 75 tsakanin watan Yulin 2023 zuwa Maris 2024 domin samar da kananan masana’antu guda 75 da ake da imanin za su kawo ci gaba da bunkasar tattalin arziki mai dorewa.
Kowanne daga cikin wadannan kamfanoni zai sami damar samun mafi girman bashi na naira biliyan daya a kan kudin ruwa na kashi tara bisa dari a kowace shekara, na lamunin dogon zango da kuma watanni 12 na jarin aiki.
Da ya juya kan mahimmancin ƙananan da matsakaitan masana'antu (MSMEs) a matsayin masu samar da ci gaba, shugaban ya bayyana matakin zuba kudi naira biliyan 125 don ƙarfafa wannan muhimmin fanni.
Daga cikin wannan kudi, Naira biliyan 50 ne za'a ware domin bayar da tallafi na sharadi ga ‘yan kasuwa miliyan daya a fadin kananan hukumomi 774 na Najeriya.
Domin magance tashin farashin kayan abinci, shugaba Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ta hada hannu da manoma da kungiyoyin su domin tabbatar da samar da abinci a farashi mai sauki.
Dangane da haka, gwamnati ta ba da umarnin fitar da ton 200,000 na hatsi zuwa gidaje a fadin kasar. Bugu da kari, za'a samar da ton 225,000 na taki da sauran kayan masarufi ga manoma da suka himmatu wajen samar da abinci a kasar.
Har ila yau, shugaban ya bayyana shirin tallafawa noman wajen samar da filayen noma 500,000 na gonaki a duk shekara.
Ya ce gwamnati za ta zuba jarin Naira biliyan 200 wajen samar da filayayen noma kimanin hekta 150,000 na shinkafa da masara da kuma na rogo kimanin hekta 100,000.
Shugaba Tinubu ya kuma ba da sanarwar wani asusun samar da ababen more rayuwa ga jihohi a fannoni masu mahimmanci kamar su gyara harkokin kiwon lafiya da na ilimi, da inganta rayuwa a karkara.
Haka kuma, Shugaban ya bayyana shirin fitar da sabbin motocin safa-safa na zirga-zirgar jama'a a fadin jihohi da kananan hukumomi.
Ya ci gaba da cewa gwamnati za ta zuba jarin Naira biliyan 100 tsakanin Yulin 2023 zuwa Maris na 2024 don samar da motoci akalla 3,000 na CNG masu kujeru 20-20, wadanda za'a raba tare da manyan kamfanonin sufuri a jihohin.
A game da jin dadin ma’aikata kuwa, shugaba Tinubu ya tabbatar wa kungiyoyin kwadago na NLC cewa, ana duba kan sabon tsarin albashin ma’aikata na kasa, tare da tanade-tanaden da za'a aiwatar da bitar albashin ma’aikata na gwamnati da masu zaman kansu.
Shugaba Tinubu ya kammala jawabin nasa da tabbatar da cewa Najeriya a yanzu tana kan turba mai kyau. Ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi imani da yadda gwamnati za ta iya cika alkawuran da ta dauka, kuma babu shakka Najeriya za ta yi nasara.
Shugaban ya jaddada cewa an riga an ceto sama da Naira tiriliyan daya tun bayan cire tallafin man fetur, wanda a yanzu za'a yi amfani da shi wajen samar da ayyuka masu amfani ga al’umma.
Yayin da al’ummar Najeriya ke ci gaba da bibiyar kalubalen tattalin arzikin da take fuskanta a halin yanzu, Shugaba Tinubu ya ce manufofinsa na da nufin aza harsashin samar da ingantaccen tattalin arziki da daidaito, wanda zai baiwa ‘yan kasa karfi da kuma tabbatar da kyakkyawar makoma ga Najeriya.
Jama’ar kasar har yanzu suna cigaba da zuba ido domin ganin yadda kudurorin da gwamnati ke ikirari da kuma matakan da ta dauka ko za su haifar da da mai ido.
Ga wani karin rahoton jawabin daga Umar Farouk Musa:
Your browser doesn’t support HTML5