A farkon jawabin nashi, shugaba Tinibu ya yi nadama da sadaukar da kansa a matsayinsa na Shugaban dake 'dauke da nauyi a wuyansa cikin gaggawa bisa la’akari da ta’addancin da zanga zangar ta haifar.
Da yake juyayin hasarar rayuka da zanga zangar ta haifar a jihohin Kano, Kaduna, Borno, Jigawa da sauran su, Shugaban yayi bayanin cewa, yayi bakin cikin warwason dukiyoyin jama’a a gidaje da manyan shaguna da ‘yan zanga zangar suka yi, bayan sun yi alkawarin cewa za a yi zanga zangar limana ne. Shugaba Tinibu ya ce rushe ‘kaddarori babu abinda zai haifar sai mayar da Najeriya baya domin kuwa da ‘dan abinda aka samu ririta za’a sake amfani da su wajen sake gina ababen da aka rusa.
Ganin irin ta’adi da ‘barnar da zanga zangar ta haifar wadda ta rikide ta zama bore da kashe kashe, da sace sace, Shugaba Tinibu yayi kira ga ‘yan zanga zangar da su dakatar da ci gaba da wannan zanga zangar nan take. Akan wannan turbar Shugaban yayi gargadi da kira ga dakarun tsaron Najeriya da su tabbatar da sun bi dukan hanyoyin da doka ta tanadar domin kare rayuwa da dukiyoyin al’umma da zummar wanzar da zaman lafiya a duk fadin kasar.
Da yake yiwa masu zanga zanga kashedi Shugaban ya bada tabbacin cewar a kullum kamar yadda akasan shi, shirye yake a tattauna domin samun maslaha maimakon fitinar da zata iya yiwa tsarin damokradiya da ake morewa zagon ‘kasa. Yana mai kira ga matasa cewa kada su bari ayi amfani dasu wajen ruguje demokradiyya.
Shugaban yayi dogon bayanın nunawa da tunatadda ‘yan ‘kasar irin yanayin da ya karbi ragamar mulkin Najeriya da suka tilasta gwamnatin daukar matakan gyara tattalin arzikin kasar. Alal misali yace janye tallafiin mai da daidaita farashin dala a kasuwar da bata da kan gado ya zama wajibi domin kawo gyara, da yake wadannan matakan na dabaibaye da kalubaloli ko wahalhalu, ya sanya gwamnati fitar da tsare tsaren kawo sauki. Yana mai cewa, matakan da na dauka sun zama dole muddin muna son mu sauya wa tattalin arzikin mu daga maras amfanar mu zuwa mai mana amfani. Ee na yarda hakan zai haifar min da kalubale amma ina tabbatar maku cewar na shirya fuskantar konwane kalubale muddin zai samadda kyakyawan shugabanci ga al’ummar Najeriya.
Shugaba Tinibu ya bayyana matakan tallafi ga jama’a musamman matasa da dilibai da manoma domin kawar da radadin gyaran tattalin arzikin da gwamnatin ke yi.
Bayan tallafi da bashi mai rangwane na musamman da aka tsarawa dalibai domin tabbatar da rashin gata ba zai hana kowanne dan Nigeria samun ilimin makarantun gaba da sakandare ba. Bisa ga wannan tsarin na NELFUND tuni ya samu Naira biliyan 45.6. Haka kuma akwai tsarin musamman na kafa cibiyoyin koyawa matasa hikimomin amfani da kimiyar zamani domin samar da ayyukkan yi inda tuni aka samu dala $620 da bisa tsari zai samar da aikin yi ga matasa miliyan 3, amma abun takaici da kunya inji Shugaban, wannan cibiyar na cikin gine ginen da ‘yan zanga zanga suka kai wa hari a kano.
Akan tsadar man fetur a sanadiyyar janye tallafin mai da shima ake kuka a kasar, Shugaba Tinubu yace gwamnati ta fara kafa cibiyoyin CNG wanda zai samar da na’urorin canza amfani da man fetur zuwa amfani da iskar gas a ababen hawa, ta yadda za’a samu rangwame a tsadar sufuri da zai samar da kaso 60% cikin dari na tsadar sufurin. Yana mai jadada cewar, kashi 80% cikin ‘dari na kudaden da ake kashewa gurin shigowa da man fetur ko dizel zai kasance an samu sauki akai.
Shugaba Tinibu ya ce, akwai dubban miliyoyin Naira da gwamnatin ta ware domin tallafa wa shirin noma ta hanyar kula da manoma a samar da kayan aikin masu rangwame bayan cire haraji akan shigowa da kayan abinci na watanni 6 domin abinci ya wadata a ‘kasar kafin kakar noman bana.
Shugaban ya kuma ce a kowanne lokaci yana tuntubar Ministoci da Gwamnonin kasar don hanzarta raba buhunan takın zamanı ga manoma na noma fiye da hecta miliyan goma yayinda gwamnonin zasu samar da gonakin noma.
A karshe, Shugaba Tinubu ya jadda cewa, ya saurari amon kukan ‘yan Najeriya musamman matasa kuma ya fahimci fushin su da bacin ran da yasa suka shiga zanga zanga kuma gwamnati na bada tabbacin cewar zata yi duk abinda ya kamata domin share hawayen su.
Saurari rahoton Umar Farouk Musa daga Abuja:
Your browser doesn’t support HTML5