Jawabin Netanyahu Ga Majalisar Dokokin Amurka Zai Ci Karo Da Zanga-Zanga

Protesters and family members of Israelis held hostage since the October 7 attack by Hamas militants hold a rally outside of the US Capitol on the National Mall on July 23, in Washington, DC.

Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu zai samu tarba daga ‘yan Majalisar Dokokin Amurka dake fama da mummunan rabuwar kai da al’ummar kasar da suka shagaltu da wasu al’amura da kuma gagarumin gangamin zanga-zanga a yau Laraba yayin gabatar da jawabi gaban majalisar a karo na 4 a tarihi

Firai Ministan Isra’ilan mafi dadewa akan mulki wanda zai gabatar da jawabi ga zaman hadin gwiwa tsakanin Majalisar Wakilai data Dattawa da misalin karfe 7 na yamma agogon gmt, ya zarta Firai Ministan Burtaniya na zamanin yakin duniya na 2 Winston Churchill, wanda ya gabatar da irin wannan jawabi har sau 3.

Benjamin Netanyahu

Ana sa ran jawabin na Netanyahu ya maida hankali kan yadda za’a ci gaba da gudanar da martanin da Amurka da isra’ila ke mayarwa ga halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya, inda ake fuskantar hatsarin yakin zirin Gaza ya fadada zuwa rikicin daka iya mamaye yankin baki daya.

Har ila yau, ana sa ran jawabin nasa ya bukaci daukar tsauraran matakai akan kasar Iran, wacce ke daukar nauyin mayakan Hamas dana Hezbollah tare da fuskantar karuwar Allah wadai.

-Reuters