Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Ja Hankalin Yan Siyasar Isra’ila Da Su Kiyayi Rura Wutar Rikici Tsakanin Su Da Palasdinu


John Kirby
John Kirby

A ranar Alhamis din nan Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ziyarci dakarun Izra’ilan a kudancin Gaza, a yayin da tankokin yakin Isra’ilan ke kara nausawa cikin Rafah. Ziyarar ta shi ta zo ne a lokacin da Netanyahu ke shirin gabatar da jawabi gaban Majalisar dokokin Amurka a Washington, cikin mako mai zuwa.

Ziyarar da ta ba da mamaki ta zo ne bayan da ministan tsaron kasa na Isra’ila Itamar Ben-Gvir ya ziyarci wani wurin ibada da ake jayayya a kan shi dake birnin kudus a rana guda.

Ofishin Netanyahu ya sanar da batun kai ziyarar bayan ya bar kudancin Gaza, inda daga bisani ya fitar da sanarwar da ta ce ‘’jajircewar da sojoji su ka yi ne ya taimaka mana samun cigaba kan yarjejeniyar sakin wadanda aka yi garkuwa da su.’’

Tun da farko, Majalisar dokokin Isra’ila, cikin sauki ta zartar da kudurin dokar da yayi adawa da kafa kasar Palasdinu.

Mai Magana da yawun Majalisar tsaron kasa na Amurka, John Kirby, yace, bai kamata yan siyasar Isra’ila su ruruta wutar fitina ba, ta ziyar da Be-Gvir ya kai zuwa masallacin Al-Aqsa.

Kirby ya kara da cewa, ‘’zamu cigaba da jan hankalin abokan huldar mu a Izra’ila da kar su yi wani abun da zai hura wutar dake ci a yanzu, ko wani abu da ka iya mara bayan tashin hankali ta ko wacce hanya.’’

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG