Sai dai, masu harakokin sufuri a Nijar da ke shan wannan man a iyaka, ko a rariya ko a tituna sun ce, ba su yi karin kudin dakon fasinja ba a hukumance, sai dai in masu motoci ne a kashin kansu su ka aiwatar da hakan.
A kan iyakar Nijar da Najeriya gefen Birni N'Konni Jahar Tahoua Jamhuriyar Nijar da Illela Jahar Sokoto Tarrayar Najeriya, farashin man fetur na bayan fage da ake amfani da shi a mafi yawan zirga-zirga ya yi tashin gwauron zabi biyo bayan janye tallafin mai da sabon shugaban kasar Najeriya ya bayyana, biyo bayan rantsuwar kama aiki a yan kwanakin da suka gabata.
Amma kuma masu sayar da man fetur na bayan fage da a ka fi anfani da shi a Nijar a iyakar kasar da Tarrayar Najeriya, na cewa abin bai gyaru ba kasancewar tsada ta yi yawa tun daga inda suke sayo shi daga Najeriya.
A cewar shugabannin kungiyoyin sufuri a garin Birnin N'Konni, basu yi karin kudin sufuri ba a hukumance, sai dai, in masu motoci ne suka yi karin kudin a kashin kansu.
Radadin janyen tallafin man fetur, ana iya cewa ya shafi harakokin kai-komo da na aikin yau da kullum da ma ayukan gonaki da na sana'o'i da dama a Jamhuriyar Nijar.
Saurari rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5