WASHINGTON, D. C. - Berlin na da sojoji kusan 90 da ke Yamai a halin yanzu. Har zuwa juyin mulki a shekarar 2023, Nijar ta kasance kawa ga kasashen yammacin duniya da ke yaki da mayakan da suka kashe dubban mutane tare da raba wasu miliyoyi da muhallansu.
Sai dai kuma mahukuntan sojan kasar sun matsawa Faransa tsohuwar mulkin mallaka da ta janye dakarunta tare da amincewa da janye sojojin Amurka, inda ta kuma kara kulla alaka da Rasha.
Ma'aikatar tsaron Jamus a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce "Jamus da Nijar sun kulla yarjejeniyar wucin gadi da za ta ba da damar ci gaba da kasancewar sojojin Jamus a Nijar," in ji ma'aikatar tsaron Jamus, inda ta kara da cewa hakan zai baiwa Berlin damar bude sansanin tun daga ranar 31 ga watan Mayu a yanzu.
Tun a shekara ta 2013 ne dai Jamus ta yi amfani da sansanin da ke Yamai a matsayin cibiyar samar da kayan aiki ga dakarunta a makwabciyarta Mali inda suke aiki a cikin tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, MINUSMA.
-Reuters