Jamus Ta Fitar Da Sunayen 'Yan Wasa Da Za Su Wakilceta A Gasar Euro 2024

An sanar da tawagar kasar Jamus da zata wakilci kasar a gasar Euro 2024, tare da dan wasan tsakiya na Bayern Munich Aleksandar Pavlovic, da dan wasan gaba na Hoffenheim Maximilian Beier da kuma dan wasan Stuttgart Chris Führich wandanda basu taba shiga wannan gasa ba lamarin da ya zo da al’ajabi.

Akwai tsoffin 'yan wasa kamar Manuel Neuer, Thomas Müller, Toni Kroos, da kyaftin Ilkay Gündogan, tawagar ta farko ta hada da abokan wasan Führich na Stuttgart dan wasan gaba Deniz Undav da ‘yan wasan baya Waldemar Anton da Maximilian Mittelstädt. Leon Goretzka, Mats Hummels da Julian Brandt sune aka dakatar da su kuma hakan ya zo da mamaki, inda babban kocin Julian Nagelsmann ya fi son Pavlovic da Robin Koch na Eintracht Frankfurt da aka ambata da farko.

Za a rage tawagar 'yan wasa 27 da za su wakilci Jamus a gasar zuwa abin da ba zai haura 26 ba ya zuwa ranar 7 ga watan Yuni, lokacin da Jamus za ta buga wasan sada zumunci na karshe kafin gasar Euro.

Nagelsmann ya tabbatar, da duk gololi masu tsaron gida hudu za su je gasar Euro, abin da ke nufin a cikin sauran ‘yan wasan ne za a dakatar da mutum daya.

Yadda Hukumar Kwallon kafa ta Jamus (DFB) ta sanar da tawagar ta haifar da kace-nace tsakanin ‘yan kasar fiye da zabo ‘yan wasa.

Ga dai teburin jerin sunayen ‘yan wasan da matsayinsu da kungiyoyinsu da shekarunsu da kuma lokutan da suka taka wa kasar Jamus leda.

* Mai tsaron gida (GK), Dan wasan baya (DWB), Dan wasan tsakiya (DWT), Dan wasan gaba (DWG):

Matsayi

Dan Wasa

Klob

Shekaru

Fitowa

GK

Oliver Baumann

Hoffenheim (GER)

33

0

GK

Manuel Neuer

Bayern Munich (GER)

38

117

GK

Alexander Nubel

Stuttgart (GER)

27

0

GK

Marc-Andre ter Stegen

Barcelona (SPA)

32

40

DWB

Waldemar Anton

Stuttgart (GER)

27

1

DWB

Benjamin Henrichs

RB Leipzig (GER)

27

14

DWB

Joshua Kimmich

Bayern Munich (GER)

29

84

DWB

Robin Koch

Eintracht Frankfurt (GER)

27

8

DWB

Maximilian Mittelstadt

Stuttgart (GER)

27

2

DWB

David Raum

RB Leipzig (GER)

26

20

DWB

Antonio Rudiger

Real Madrid (SPA)

31

68

DWB

Nico Schlotterbeck

Borussia Dortmund (GER)

24

11

DWB

Jonathan Tah

Bayer Leverkusen (GER)

28

23

DWT

Robert Andrich

Bayer Leverkusen (GER)

29

3

DWT

Chris Fuhrich

Stuttgart (GER)

26

3

DWT

Pascal Gross

Brighton (ENG)

32

5

DWT

Ilkay Gundogan

Barcelona (SPA)

33

75

DWT

Toni Kroos

Real Madrid (SPA)

34

108

DWT

Jamal Musiala

Bayern Munich (GER)

21

27

DWT

Aleksandar Pavlovic

Bayern Munich (GER)

20

0

DWT

Leroy Sane

Bayern Munich (GER)

28

59

DWT

Florian Wirtz

Bayer Leverkusen (GER)

21

16

DWG

Maximilian Beier

Hoffenheim (GER)

21

0

DWG

Niclas Fullkrug

Borussia Dortmund (GER)

31

15

DWG

Kai Havertz

Arsenal (ENG)

24

44

DWG

Thomas Muller

Bayern Munich (GER)

34

128

DWG

Deniz Undav

Stuttgart (GER)

27

1