A cewar hukumar kwallon kafar Saudiyar, an ci tarar kyaftin din Al-Nasr kuma tsohon tauraron kungiyar Porto riyal dubu 30 kwatankwacin dalar amurka dubu 8 saboda aikata laifin, wanda ya saba dokar hana tsokanar ‘yan kallo yayin wasan kwallon kafa.
Babu damar daukaka kara akan wannan hukunci.
Wani faifan bidiyo ya bayyana wanda ke nuna Ronaldo yana tura dan yatsa kusa da marainansa a matsayin martani ga tunzurawar da ‘yan kallo ke masa ta hanyar rera sunan dadeddan abokin hamayyarsa a harkar kwallon kafa, Lionel Messi, a fafatawar da Al-Nasr ta tashi ci 3-2 tsakaninta da kungiyar kwallon kafar Al-Shabab.
Cikin kankanin lokaci faifai bidiyon ya yadu harma ya mamaye batutuwan da aka fi tattaunawa akansu a kafafen sada zumuntar saudiya.
Jaridar harkokin wasanni ta al-riyadiya ta ruwaito Ronaldo na cewar yana mutunta dukkanin kungiyoyin kwallon kafa kuma alamar daya nuna ta bayyana karfi ce da samun nasara-ba wai don aikata laifi ba-kuma an amince da hakan a nahiyar turai.
Dandalin Mu Tattauna