Me magana da yawun Juventus ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Afp cewar, an sanarda kungiyar kwallon kafar game da hukuncin da aka zartar akan tauraron dan wasan mai shekaru 30 daya taba daukar Kofin Duniya, wanda tun a watan Satumbar bara aka yi masa dakatarwar wucin gadi.
A cewar me magana da yawun kungiyar ta Juventus, “sai a safiyar yau muka samu sanarwar.” kotun hukunta shan kwayoyin kara kuzarin tsakanin ‘yan wasa ta Italiya bata badai martani da wuri ba sa’ilin da Afp ya tuntube ta.
Masu shigar da kara na kotun sun bukaci a kakabawa tsohon dan wasan tsakiya na kungiyar Manchester United tukunkumin hana taka leda na shekaru 4, wanda aka gano sinadaran kara kuzari a jininsa a yayin wasan Juventus na farko a gasar Serie A ta bara inda suka fafata da Udinese a ranar 20 ga watan Agustar daya gabata.
Bayan wata guda da dakatarwar da aka yiwa Pogba ta wucin gadi, gwaji na 2 ya tabbatar da samun sinadaran ''testerone'' a cikin jininsa.
A cewar wakilin Pogba, an samu sinadarin testerone din a cikin jininsa ne sakamakon amfani da kwayoyin abinci masu kunshe da magani ko “food supplement” a likitance da wani likita daya gani a Amurka ya rubuta masa.
Dandalin Mu Tattauna