Jamuriyar Nijar Ta Kori Wasu Kananan Jakadunta Daga Aiki

Sojojin CNSP da suka yi juyin mulki a Nijar

Hukumomin mulkin sojan Jamhuriyar Nijar sun kori wasu kananan jakadun da ke wakiltar kasar a kasashe da dama na nahiyar Turai da Asia har ma da na kasashen Afrika.

Koda yake ba a bayyana dalilan daukan wannan mataki ba, masana sha’anin diflomasiya na fassara abin a matsayin mai nasaba da sabuwar tafiyar da kasar ta sa gaba bayan juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2023.

Kananan jakadun wato Consuls Honoraires kimanin 26 ne ma’aikatar harkokin wajen Nijar ta bada sanarwar kora daga aiki kamar yadda ya ke rubuce a wata takardar jerin sunayensu da kasashen da suke da ofishin a matsayin wakilan wannan kasa.

Ba a dai yi karin haske game da dalilan daukan wannan mataki da ba kasafai ake ganin irinsa a Nijar ba, illa kawai sanarwar hukumomin ta yi tunatarwa game da kafuwar Majalissar CNSP da nadin Fira Minista Shugaban gwamnati da kuma yarjejeniyar birnin Vienne ta watan Afrilun 1963 da ke fayyace ka’idodin da suka shata huldar kasashe da ta aikin kananan ofisoshin jakadanci.

A hirarsa da Muryar Amurka, masani kan harkokin huldar kasa da kasa Moustapha Abdoulaye, ya yi karin bayani kan fassarar da za a iya yi wa irin wannan mataki a diflomasiyance, jerin sunayen wadanan kananan jakadu na nunin alamar galibinsu ba ‘yan kasar Nijar ba ne dalili ke nan na sake bsu.

Wadanan kananan jakadu da hukumomin mulkin sojan Nijar suka kora sun hada da jami’an da ke wakiltar kasar a wasu kasashe 6 na Afrika sai jami’ai 13 da ke wakilci a kasashen turai, yayin da wasun ke wakilcin Nijar a kasashe 7 na Asia.

Saurari rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Nijar Ta Kori Wasu Kananan Jakadunta Daga Aiki