Jam'iyyar APC mai mulki da PDP mai adawa, sun rage magana kan batun sauya sheka to ya rasa kujerar sa.
Ba mamaki hakan na da nasaba da yadda kowanne sashe ya amfana daga sauya shekar.
Yayin da PDP ta koma kare shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da wadanda su ka sauya sheka zuwa adawa, ita kuwa APC na kare tsohon shugaban maras sa rinjaye Godswill Akpabio.
Gabanin komawa zaman majalisar dokokin da ba mamaki sai 25 ga watan gobe, PDP na nuna sam ba za ta lamunci tsige shugaban majalisar dattawan Bukola Saraki ba; wanda APC ta bukaci wa imma ya yi murabus, ko ta tsige shi da samun karin 'yan majalisa bayan zaben cike gurbi a Bauchi da ya kawo Yahaya Gumau, da a Katsina da ya kawo Ahmed Babba Kaita.
Shehu Yusuf Kura kakakin shugaban jam'iyyar PDP, ya ce ai shugaban majalisar zaben sa a ka yi kuma har yanzu ya na da goyon bayan da ba za a iya tsige shi ba.
Bayan sauya shekar da gwamnan Binuwai Samuel Otom yayi zuwa PDP an yada jita-jitar wai gwamnan Plateau Simon Lalong, da ke makwabtaka zai bi sahu.
Wannan ya wakilin Sashen Hausa Nasiru Adamu El-Hikaya ya tambayi Gwamna Lalong menene matsayin sa kan rade-radin?
Za a fi gane alkiblar 'yan siyasar Nigeria bayan zaben fidda gwanin jam'iyyun da za a kammala mikawa hukumar zabe sunayen a watan Disamba.
A saurari rahoton Nasiru Adamu El-Hikayya
Your browser doesn’t support HTML5