Tunda guguwar canza sheka ta kada a Nigeria, musamman yadda wasu sanatoci suka bar jam'iyyar APC zuwa PDP, rikici ke tashi a majalisar dattawan kasar.
Rikicin ya samo asali ne daga APC wadda ake zargin tana yunkurin tsige shugaban majalisar Dr. Bukola Saraki daga kan mukaminsa. Saboda haka ne 'yan PDP suka lashi takobin kwana cikin majalisar har sai sun ga abun da ya turewa Buzu nadi.
Dan majalisa mai wakiltar Pankshin, Kanke da Kanam cikin jihar Plato, Timothy Ngolu, yana cikin wadanda suka ce zasu ci gaba da kwana cikin majalisar. A cewarsa yayinda suke aikin kwamitinsu sai jami'in dake daukar sandar ikon majalisar ya fada masu wasu 'yan majalisar sun iso. Wai sun zo ne su yi zama a majalisar da zummar yin juyin mulki, kenan su nada wasu shugabannin majalisar.
Sai dai wani dan jam'iyyar APC mai wakiltar Chanchaga ta jihar Niger Muhammadu Umaru Bago, ya bugi kirji yana cewa har yanzu jam'iyyarsu ce ke da rinjaye a majalisun biyu kuma duk wannan kace-na-ce ya samo asali ne tun daga lokacin da Shugaba Buhari ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takarar shugaban kasa. Ya ce suna gwagwarmaya ne domin tabbatar da shugabanci nagari a kasar. A cewarsa cikin majalisu da ma kasa gaba daya duk wanda ya ce bai yadda da Shugaba Buhari ba, a cikin biyu akwai daya. Walau da can shi dan adawa ne na PDP ko kuma dama yana cikin APC ne amma ya san babu inda zai je. Ya kara cewa da yardar Allah a zabe mai zuwa zasu ninka kuri'un da suka samu a zaben 2015.
A nan Timothy Ngolu ya ce idan har APC na da karfin gwuiwa haka sai su bi doka. Ya ce me ya sa ba za su bari sai lokacin da majalisa ta bude sannan su kawo kudurinsu ba. Idan ba'a son Bukola Saraki ba sai a ciresh ba. Ya ce yanzu suna hutu kuma doka ta ce wanda ya bada hutun shi ne kadai zai iya bude majalisar. Suna kokarin maimaita irin abun da ya faru ne a Binuwai. A cewarsa ba zasu bari hakan ya faru ba.
A saurari rahoton Medina Dauda domin karin bayani
Facebook Forum