Jami'an Tsaron Somaliya Sun Dakile Hari Kan Gidan Yari

Nyu-York

Jami’an tsaron kasar Somalia sun dakile wani yunkurin kai hari gidan yarin da aka tsare mayakan Al-shabab dake birnin Mogadishu babban birnin kasar.

A kalla mutane goma sha daya suka mutu bayanda jami’an tsaron kasar Somalia suka dakile wani yunkurin kai hari gidan yarin da aka tsare mayakan Al-shabab dake birnin Mogadishu.

Al-Shabab ta dauki alhakin harin da aka kai yau Lahadi kan gidan yarin dake karkashin ma’aikatar leken asirin kasar Samaliya.

‘yan bindiga sun kai hari kan gidan yarin ne bayanda bom ya tarwatse a wata mota bakin kofar shiga gidan yarin. Shaidu sun shaidawa Sashen Somali na Muryar Amurka cewa, dakarun tsaron sun kashe dukan maharani kuma babu ko fursuna daya da ya tsere.

Kakakin ma’aikatar tsaron Somaliya Mohammed Yusuf Osman yace wadanda suka rasu sun hada da farin kaya daya da jami’an tsaro uku da kuma mayakan al-Shabab bakwai.

A cikin shekaru hudu da suka shige, rundunar wanzar da zaman lafiya ta Kungiyar hadin kan Afrika da kuma dakarun gwamnatin kasar Somali sun kwace wurare da dama dake karkashin kungiyar mayakan da ake alakantawa da al-Qaida, sai dai har yanzu kungiyar tana ci gaba da barazana ga zaman lafiya da dorewar kasar Somaliya.

Mayakan kungiyar sun kashe ‘yan majalisar dokokin kasar Somaliya shida cikin wannan shekarar, suka kuma kai hari a fadar shugaban kasar