Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Jamhuriyar Niger tun da Dadewa Harkokin Ilimi Suka Tabarbare


Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar
Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar

Ayar doka mai lamba 12 ta kundun tsarin mulkin kasar Niger ta dorawa gwamnati nauyin baiwa 'yan kasar ilimi amma shekaru da dama kenan da harkokin ilimi suka shiga halin ni'yasu.

Rahotanni na nuni cewa kowace safiya matsalar ilimi sai kara kamari ta keyi a kasar. Batun samun ingantacen ilimi na samun barazana ga al'ummar kasar wanda kidigdiga tace sun haura mutane miliyan goma sha shida.

Yawan yaje-yajen aiki da batun kasafin kudi a fannin ilimi da rashin cika alkawura da gwamnatin ke daukarwa malaman makarantu suna cikin kadan da ke kawowa harkokin ilimi tarnaki.

Amma wasu masana a fannin ilimi suna ganin ta ran gini ake zane domin tun lokacin da wasu hukumomin kasashen duniya suka gindaya wasu sharuda ga Niger yasa harkokin iliminta suka fara tabarbarewa.

Lamarin yasa har yanzu tamkar kasar tana cikin mulkin mallaka ne a harkokin ilimi. Kasar tana cikin danniya domin har yanzu Faransa bata saki kasar ba bata yaye kasar ba ta samu ta zauna da duwawunta kafin ma ta tashi ta tsaya kan kafafunta ta kuma yi tafiya dasu.

Idan gwamnati ta cigaba da yin aiki da sharudan da kasashen duniya da bankin duniya ke tsara mata to kullum tana cikin matsala.

Bincike ya nuna cewa yadda da sharudan da kasashen waje suka tsara ta sa kasar ta fara ja baya a fannin ilimi tare da rage kaso da suke baiwa wannan fannin. Bukatoci sun karu amma kuma dole gwamnati ta rage daukan malamai a guraben aiki tare da maye gurbinsu da 'yan kwangila wadanda yanzu haka su suka mamaye kashi tamanin cikin dari na malaman dake koyaswa a makarantun bokon Niger. Yawan 'yan kwantiragin ya sa kowane lokaci su ke barazana ko kuma su shiga yajin aiki sakamakon rashin cika alkawuran da gwamnati ta dauka na shafe masu hawaye.

Malam Munkaila Halidu jigo ne a cikin kungiyoyin. Yace gwamnati tayi alkawarin zata dauki 'yan kwantiragi su yi aikin din-din-din amma ba'a yi hakan ba. Firayim ministan kasar yayi alkawarin cewa za'a dauki malamai aikin din-din-din tun shekarar da ta wuce. Akwai alawus da gwamnati bata bayar ba. An yiwa ma'aikatan gwamnati karin albashi amma banda malaman makarantu. Lamarin ya sa alkawura suna tarar da wasu alkawura a koyaushe wadanda gwamnatin bata cikawa. Cikin alkawuran har da daukewa iyaye dawainiyar 'ya'yansu daga haihuwa har zuwa shekaru goma sha shida. Wadannan abubuwa suka sa malaman suna ja-in-ja da gwamnati kusan kowane lokaci.

Amma malam Abdu Kawu mai bada shawara a ofishin ministan ilimin kasar yace kowa yayi imanin akwai matsaloli. Duk inda aka taba harakar ilimi akwai matsala. Ko ba'a yi yajin aiki ba ana cikin matsala. Ya dace yanzu a san matakan da za'a dauka a tsayar da yajin aikin da malaman makaranta kan yawan shiga. An yi abun da za'a iya yi kuma ana cigaba da yi amma ba za'a iya yin duk abubuwa ba gaba daya rana daya. Za'a dauki lokaci.

Ga cikakken rahoton Abdullahi Mamman Ahmadu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:52 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG