Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jamhuriyar Niger Ta Dauki Matakan Rigakafin Cutar Ebola


Hannun wanda ya kamu da cutar ebola
Hannun wanda ya kamu da cutar ebola

Daga manyan tashoshin motoci da iyakokin kasar da filayen jiragen kasa suna cikin halin ko ta kwana game da binciken kwakwaf domin gano wani dan kasa ko bako dake da niyyar shigowa kasar amma yana dauke da cutar ebola.

Daukan matakan sun biyo bayan bayyanar cutar ne a wasu kasashen Afirka dake da dangantaka ta kud da kud da kasar ta Niger musamman ma tarayyar Najeriya.

A safiyar jiya ne ministan kiwon lafiya na kasar Mani Agali yayi hadin gwiwa da babban mai shiga tsakani ta kasar ta Niger Shehu Ahmadu. Tare suka kai wata ziyara a wasu wurare domin gane ma idanunsu yadda binciken yake gudana.

A filin saukar jirgin sama dake Niamey duk wasu matakan bincike an daukesu. Da zara mutum ya sauka daga jirgin sama jami'an zasu tambayeshi sunashi daga inda ya fito da kuma inda zashi. Idan mutum na tari ko yana da masassara ko ciwon kai sai a wareshi gefe guda.

Kawo yanzu babu wani dan kasar da ya kamu da cutar amma sun dauki shirin ne saboda kare kasar da al'ummarta daga mummunar cutar mai kisa da gaggawa fiye da kima.

Ga rahoton Abdullahi Mamman Ahmadu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:09 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG