Jamian Kwastam Sun Harbe Wani Matashi

  • Ladan Ayawa

Kasauwar Kwastan na Maiduguri, bashida nisa da fadan Shehu, inda ‘yan Boko Haram ke shawaginsu kafi ‘yan sibiliyan JTF da sojoji su koresu 26 ga Mayu.

A cewar shaidun gani da ido sunce matashin ya dauko shinkafa ne daga jamhuriyar Niger inda ya tsallako ta kan iyakar Illela amma kuma jamiaan kwastan suka tsare shi a wani shingen binciken su dake asara dake cikin karamar hukumar mulki ta Gwadabawa.

To sai dai marigayin mai suna Shaibu yaki ya tsaya abinda yasa Jamian na kwastan suka biyo shi zuwa tungan kwangi, inda daya daga cikin su ya daga bindiga ya harbe shi dai-dai idanun sa.Lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar sa kai tsaye.

Lawali Gwadabawa shine mahaifin matashin da aka harbe.

‘’Ina nan zaune kawai sai aka ce mani kwastan sun biyo yaro sun harbe shi, kawai sai naga yara sunzo suna kuka wai ya mutu, sai na tashi zuwa asibiti domin inga inda yaro na yake, sai aka ce mani wai anyi sokoto dashi, aka ce mani in dawo in zauna, na zo na zauna sai ga mota ta kawo mani gawar sa, ba wani Jamiin kwastan da yazo nan gida na amma, ‘yan sanda sunzo sunyi mani taaziyya.Kuma ni an bide ni in tafi can C I D Office nazo CID office ance mani na dan saurara za a bidar mani hakki na game da wannan kissan gillar da akayi wa Yaro na na ganganci saboda ban san laifin da yaro na yayi ba wanda aka tafi aka kashe shi.Abinda nake so duk yadda ta kasance mahukunta su bi mani hakki na, idan kashe wanda ya kashe shi za ayi to a kashe shi.’’

Sai dai da wakilin sashen Hausa Murtala Faruk nSanyyina ya tuntubi shugaban hukumar Kwastan mai kula da jihohin Sokoto, Kebbi da Zamfara Sani Madugu ya tabbatar da faruwar Lamarin ga kuma abinda yace.

‘’Wannan abu bai muna dadi ba kuma ba aikin kwastan bane mu kashe mutane, mu bamu je kan titi ba domin mu kashe kowa ba kuma wannan abu bamu dadin sa ba, dan haka ne ma muka tattara duk kwastan dake wannan wurin da wannan abu ya faru muka mika su ga hukumar ‘yan sanda domin tayi bincike’’

Ga Murtala Faruk Sanyinna da Karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Jamian Kwastan Sun Harbe Wani Matashi 2'58