Da yake bayanin yadda aka damke mutanen kwamandan birget na 33 birgediya janal Abraham Luka Dusu, yace hadin gwiwar rundunar soji dake Gwambe da kuma na garin Jos ne suka kame mutanen.
Rundunar ta kama mai suna Victor Moses, wanda ya shaida cewa yana daga cikin mutanen da sukayi nasarar tayar da bom a garin Madalla ta jihar Neja. Kamun da akayiwa Victor ya biyo bayan yunkurin da yayi nay a shiga masallaci a garin Alkaleri, inda yace yana son ya musulunta ne amma mutanen garin basu amince da bayanin da yayi musu ba, sai suka kaiwa soja rohoto.
Victor Moses bayyana sauran ‘yan leken asirin Boko Haram wanda suka hada da Abubakar Shatima da Salisu Mohammed Bello da kuma umar Sadiq Madaki, dukkanninsu a garin Gombe. Bayan an kammala binciken farko za a dauki mutanen hudu zuwa Maiduguri cibiyar bincike na soji domin a ci gaba da yi musu tambayoyi.