Jami'ai Sun Tuhumi Mutumin Da Ake Zargi Ya Kai Hari New York

Ahmad Khan Rahami

Jami'ai a Amurka sun tuhumi mutumin da ake zargi da kai karin bam, haifaffen kasar Afghanistan Ahmad Khan Rahami, tuhumar ta hada da dana jerin bama-bamai a New York da New Jersey cikin kwanaki uku da su ka gabata, a wani al'amari na ta'addanci.

Tuhume-tuhumen da ake ma Rahami sun hada da wani zargi cewa ya yi yinkurin amfani da makami mai barnar gaske.

Dama an tuhumi matashin da yinkurin kisa, saboda musayar wutar da ya yi da 'yan sanda a New Jersey. A yanzu ya na asibiti, inda ya ke murmurewa daga harbinsa da aka yi da bindiga lokacin da ake kokarin kama shi.

Labarin tuhumar matashin mai shekaru 28 da haihuwa, ya biyo bayan bayanin hukumar bincike ta FBI tun da farko a jiya Talatar, cewa ta yi ta nazarin take-taken Rahami shekaru biyu da su ka gabata, to amma ba ta samu cikakkun hujjoji na kaddamar da fadadadden bincike a kansa ba.

Hukumar ta FBI ta ce ta gudanar da bincike kan Rahamin a 2014 ne, bisa ga bayanan da mahaifinsa ya rada mata, wanda ya ce shi fa ya damu da yiwuwar alaka tsakanin dansa da wasu masu tsattsauran ra'ayi.

Hukumar ta ce, to amma a yayin ganawarsa ta gaba da masu bincike, sai mahaifin, wato Mohammed Rahami ya canza labarinsa, ya ce ya damu ne saboda ganin yadda dansa ke hulda da wasu 'yan iska da miyagu. Hukumar ta FBI ta ce sai ta yi nazarin harkokin dan, amma ba ta ga wani dalili na kaddamar da bincike mai zurfi ba.

Lokacin da hukumar ta FBI ke binciken a 2014, Rahami na tsare saboda zargin ya daba ma dan'uwansa wuka.