Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar FBI Tayi Taron Manema Labarai Akan Bam da Ya Tashi A Birnin New York


Ahmad Khan Rahami wanda kuma tuni ya shiga hannun jami'an tsaro
Ahmad Khan Rahami wanda kuma tuni ya shiga hannun jami'an tsaro

Kwana daya kafin a bude taron Majalisar Dinkin Duniya ko MDD sai kwatsam wani bam ya tashi a cikin birnin New York, birnin dake dauke da hedkwatar MDD din

Amma ba a wurin taron ne bam din ya tashi ba kuma tuni jami'an tsaro suka samu nasarar cafke Ahmad Khan Rahami wanda ya aikata danyen aikin.

Kodayake mutane sun jikata sanadiyar bam din amma babu wanda ya rasa ransa kuma wasu ma cikinsu har sun fara murmurewa. Shi ma Ahmad Rahami yana asibiti saboda rauni da ya samu yayinda yake fafatawa da jami'an tsaro.

Hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka ko FBI da wasu jami'an tsaro sun yiwa manema labarai karin haske a taron da suka kira domin fadakar da jama'a. Sun bayyana abun da suka yi da kuma su keyi domin tantance dalilin aikata wannan aika-aikar. Sun ce zasu gano duk wadanda suke da nasaba da tashin bam din.

Magajin birnin New York B. Bilassio na cikin wadanda suka yi jawabi a wajen taron. Yace komi na hannun 'yansanda wadanda suke bincike kuma zasu hada kai dasu domin gano gaskiyar lamarin da zummar kare birnin daga hannun 'yan ta'ada.

Gidan sayar da abinci na su Rahami da hukumar FBI take kyautata zaton nan ne aka shirya aiwatar da ta'asar
Gidan sayar da abinci na su Rahami da hukumar FBI take kyautata zaton nan ne aka shirya aiwatar da ta'asar

Kwamishanan 'yansandan birnin yace ba zasu yi kasa a gwuiwa ba wajen binciken. Ya kira jama'a da su taimaka wajen tabbatar da tsaro. Yace da zara ka ga abun da baka yadda dashi ba ka shaidawa jami'an tsaro domin kada a cuci jama'a. Yace suna cigaba da binciken wanda suka kama.

Ga rahoton Ladan Ibrahim Ayawa da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:41 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG