A jawabinsa na karshe ga zauen babban taron Majalisar Dinkin Duniya ko MDD a takaice a zaman shugaban Amurka yau Talata, Mr. Obama ya bada misali da durkushewar doka da oda a yankin gabas ta tsakiya, yace "al'umomi" suna zaman rashin tabbas da fargaba.
Shugaban na Amurkan ya ci gaba da cewa "muna ganin gwamnatoci suna hana 'yan jarida yin aikinsu. Kungiyoyin 'yan ta'adda suna amfani da kafofin sadarwa wajen gudanar da wankin kai ga matasa, ta haka suke jefa al'uma cikin fitina, wanda hakan yake janyo mutane su fusata kan 'yan ci rani da bakin haure, da muslmi wadanda basu aikata ko wani laifi ba," inji shugaban.
Tunda farko babban sakataren na MDD Ban Ki-moon yayi jawabi na kaddamar da zaman zauren na bana.