Shugaban Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Najeriya (NDLEA), Burgediya Janar Buba Marwa mai ritaya, ya amince da daga likafa ta musamman ga wani sufurtandan yaki da kayan maye mai suna, Francis Igonoh, bayan data bayyana cewar shine ya lashe kyautar Kwalejin Horas da Tursasa Bin Doka ta Duniya (ILEA) akan yin fice wajen aiwatar da aiki.
Da yake sanar da karin girman da aka yiwa jami’in a wani kwarya-kwaryan bikin da Francis Igonoh ya mika shaidar kyautar daya lashe ga Shugaban Hukumar ta NDLEA, Buba Marwa ya yaba mishi saboda sanya hukumar dama Najeriya alfahari a idon duniya.
A cewar Marwa, hakan tasa NDLEA ke alfahari da jami’anta, kuma take girmama irin kwazon da suke nunawa, inda ya kara da cewar hukumar zata cigaba da sa idanu akan irin kokarin jami’anta, tare da sakawa kwazo da aiki tukuru.
Marwa ya cigaba da cewar jami’in ya samu karramawar duniya ne saboda jajircewa da kwazon aiki da kuma kwarewa, inda yace ya amince da daga likkafarsa zuwa mukamin mataimakin kwamandan yaki da kayan maye kasancewar dama lokaci yayi da za ayi masa karin girma zuwa matakin babban sufurtandan yaki da kayan maye, domin kara karfafa masa gwiwa tare da sauran abokan aikinsa.
Takardar shaidar mai dauke da sa hannun Daraktan, Shiyar Afrika ta Yamma na cibiyar bada horon, Harward Lampley, ta yabawa jami’in hukumar ta NDLEA, inda tace an karrama shi a bisa cancancta.